Da Dumi Dumi

’Yan sanda sun aika wa Ala takardar sammaci

Rahotanni da muke samu ya nuna cewa rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta aika wa Aminu Ala takardar sammaci.

Takardar sammacin wanda Aminiya ta samu ta nuna cewa rundunar ’yan sandan na bukatar Ala ya zo ofishin ’yan sandan a ranar 2 ga watan Satumba domin amsa wasu tambayoyi.

Ga takardar sammacin a kasa:

 

Wasu suna ganin gayyatar ba ta rasa nasaba da siyasa, kasancewar takardar ta bukaci Alan ya je wajen jami’in ’yan sanda mai kula da harkokin siyasa.

ADVERTISEMENT
Share