Aminiya

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda ke da gidan Horon Matasa a Rigasa a jihar.

Aminiya ta bayar da labarin wani samame da rundunar Yan Sandan suka kai gidan horon matasan a ranar Asabar sannan suka yi awon gaba da shi mai gidan tare kuma da kwashe matasa 147.

ADVERTISEMENT

Sai dai wakilinmu ya gana da shi Malam Niga din a ranar Lahadi da yamma inda ya tabbatar da bada belin nasa da ‘yan Sandan suka yi a ranar Asabar da yamma.

” Eh, an sako ni a jiya ( Asabar) da yamma kuma a yanzu haka ina gida,” inji shi ta wayar tarho

ADVERTISEMENT

Aminiya ta kuma gan‎a da kakakin Rundunar Yakubu Sabo, domin jin karin bayani inda shima ya tabbatarwa da wakilinmu cewa, an bada belin Malamin.

” Am bada belinsa a ranar Asabar da yamma amma fa zai dawo gobe Litinin,”‎ in ji shi.

Sai dai har yanzu gwamnati ba su mayar da matasan da aka kwashe gidan ba saboda suna can sansanin Alhazai na Mando inda aka ajiyesu ana Kula da su kafin iyaye da yan’uwa suje a karbe su.