Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan sanda sun bayyana shaidu 14 a Kotun Zabe ta Kano

Kwamishinan ’Yan sandna Jihar Kano Ahmed Iliyasu ya gabatar da takardu 14 a matsayin shaida a gaban Kotun Saurarren Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kano.

Takardun da ’yan sandan suka gabatar suna daga ckin takardu 61 da masu kara da suka hada da Jam’iyyar PDP da dan takararta Abba K. Yusuf suka nemi ’yan sandan su gabatar a gaban kotun.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan ’Yan sandan wanda ya samu wakilcin jami’i a Sashen Shari’a na Rundunar, Sufiritanda Sunday Ekwe ya gabatar da takardu 14 da kwafen takardar sakamakon zaben da aka gudanar ne da aka ba ’yan sandan tunda farko.

Sai dai wadanda ake kara da suka hada da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Jam’iyyar APC sun ki amincewa da takadun da aka gabatar a gaban kotun.

ADVERTISEMENT

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya, kotun ta aike da takardar samamci ga Rundunar ’Yan sandan don gabatar da takardu 61 da suke hannunta.

A wani labarin kuma Shugaban Jam’iyyar PDP Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya shaida wa kotun cewa jam’iyyarsa ta PDP ita ke kan gaba a zaben da aka gudanar a ranar 9 ga Maris har a mazabar Gama da ake rigima a kanta wanda hakan yake nuni da cewa babu bukatar a gabatar da wani zaben cike- gurbi.

Sai dai lauyan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa tambaya cewa ko yana sane cewa an dauke sakamakon mazabar Gama? A nan ne Shugaban PDP din ya bayyana cewa “Ai abin da suke ta fada ke nan sai dai ni ejen dina a wannan mazaba ya shaida min cewa takardun sakamakon suna nan daidai babu wanda ya bace.”