✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke mutum 6 kan laifukan zabe a Benuwai

Rundunar ta ce ba za ta ragawa masu shirin tada yamutsi a zaben da ke tafe a jihar ba.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwai, ta ce ta kama mutum shida da laifuka daban-daban na zabe a zaben shugaban kasa da na ’yan majalisun tarayya da aka kammala a jihar.

Kakakin rundunar, SP Catherine Anene ce, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Makurdi.

Kwamishanan ’yan sandan Jihar Benuwe, CP Wale Abass, ya yaba wa jami’an da suka kama masu laifin a lokacin zaben.

Ya bayyana cewa mutum shidan, ana ake zargin su da laifin mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, da kwace akwatunan zabe da kuma mallakar katin zabe guda tara ba bisa ka’ida ba.

“A cewar CP, an kammala bincike, an kuma aike da takarda ga hukumar zabe, domin ci gaba da daukar matakin da ya dace.

“Ama kuma gargadin masu laifin zabe da su guji irin wannan rashin bin doka da oda domin hukuma ba za ta raga musu ba,” in ji ta.

Ta kara da cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, ya umarci kwamandojin ’yan sanda na sassan jihar da su tabbatar an gudanar da zabukan cikin lumana a yankunansu a ranar Asabar.