✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ce sun taka sawun ’yan fashi ne a Bauchi

Rundunan ’Yan sandan Jihar Bauchi ta musanta zargin da aka yi wa jam’ianta na hannu a wani fashi da makami da ake yi a hanyar…

Rundunan ’Yan sandan Jihar Bauchi ta musanta zargin da aka yi wa jam’ianta na hannu a wani fashi da makami da ake yi a hanyar Dambam zuwa Kano a Karamar Hukumar Dambam da ke Jihar Bauchi inda aka yayata wani faifan bidiyo da aka dauka lokacin da aka kori ’yan fashin.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Phillip S. Maku ya musanta labarin faifan bidiyon da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani da ke nuna yadda ’yan sanda ne ke yi wa al’umma fashi a wani taron gaggawa na manema labarai da ya kira a Bauchi.

Maku ya ce kodayake an yi fashi da makami amma yadda ake yayata labarin karya ce kuma yunkuri ne na a bata musu suna, saboda ’yan sanda sun je wajen ne don su taimaki jama’a, amma jama’a suka far musu har suka suna kokarin jikkata su, sai suka gudu suka bar motarsu da wayar wani dan sanda.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa motar da ake yadawa a faifan ta ’yan sanda ce, amma sun je wajen ne taimakon jama’a, ya kuma bada tabbacin cewa suna binciken faifan bidiyon, kuma suna gudanar da bincike domin gano hakikanin gaskiyar lamarin, kuma za su sanar da jama’a da zarar an kammala.

’Yan sandan sun gabatar wa ’yan jarida wakilin Hakimin Dambam, Lamido Musa Sulaiman da wani direba da lamarin ya faru a idonsa Umar Muhammad daga Jihar Kano, wadanda suka tabbatar da cewa ’yan sandan sun je taimako ne mutane suka far musu.

Wani mazauni garin Dambam da ya ce sunansa Bala Mato cikin hirarsa da ’yan jarida ta wayar tarho ya yi zargin cewa ’yan sandan sun fita aikin sintiri ne sai suka buge da kwanta-kwanta, suka kada mota suka debe atamfafofi da yadudduka da ta debo, daga cikin motar da suka kayar suka loda a tasu. Ya ce bayan sun kwabe kayansu sun lullube kansu sun bar wayoyinsu da bindigoginsu a cikin motarsu, sai suka fara fashi karo na biyu, kuma suna cikin yi  ne sai ga wata motar ta zo, sun fara yi musu sai suka harba bindiga sai suka gudu suka bar motarsu da wadannan kayayyaki da suka yi fashi, har ma sun ji wa wani jariri rauni.

Ya ce shi ne daya daga cikin direbobin suka jawo motar da kayan da suka loda a cikin yanzu haka motar tana kofar Hakimin Dambam.

Jami’in Hulda da Jama’a na Karamar Hukumar Dambam, ya fayyace abin da ya gani da idonsa inda ya ce “Mota ta farko da ta zo an tare ta kuma an bubbugi mutane an sari wadansu mun ga masu rauni mutum takwas ciki har da karamar yarinya, ana cikin yin fashin ne wadansu ’yan kasuwa a jere a kananan motoci kusan goma, suka iso wurin mutanen.”

Ya ce sun ce ina mutanen suke, suka ce sun gudu amma mutum uku sun zo wajensu da bindiga suka ce za su taimake, suka ce ba su yarda da su ba. Kuma suna tsaye haka sai wadansu mutum biyu suka zo su ma suka ce sun zo ba su taimako ne. Sai suka tambaye su su wane ne su, sai suk ga ce ’yan sanda ne alhali  ba su khaki babu bindiga, sai suka ce musu “Ku ne kuka yi mana wannan fashi shi ne ke nan kuka biyo, sai suka tafi su kuma daga wajen suka tattara duk abin da yake wajen suka kawo gidan Sarki cikin motar. Ya ce an samu bindiga da harsasai biyar da sanduna itatuwa irin na dukan mutane a cikin bayan motar da kuma sanduna.