✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun ci zarafin wakilin Radiyo Iran a wajen shari’ar Zakzaky

An samu wata ‘yar hatsaniya tsakanin ‘Yan sanda biyu da wakilin gidan radiyon Iran mai Suna Aliyu Muhammad, a lokacin da ‘yan Sandan suka bukace…

An samu wata ‘yar hatsaniya tsakanin ‘Yan sanda biyu da wakilin gidan radiyon Iran mai Suna Aliyu Muhammad, a lokacin da ‘yan Sandan suka bukace shi da ya bar harabar kotun da ake shari’ar shugaban Kungiyar IMN Shaikh Zakzaky a Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na safe a lokacin da ake gudanar da shari’ar Shaikh Zakzaky a babban Kotun jihar.

Aliyu ya shaidawa Aminiya cewa, abin ya bashi mamaki matuka yadda yaga ‘yan Sandan suka nace wai dole sai ya bar aikin da yake yi a wajen domin basu san ganinshi a kotun.

“Basu fadamin dalilinsu na san in bar harabar kotun ba, duk kuwa da ina tare da sauran ‘yan jaridu amma ni kadai kurum suka bukaci da sai na bar wurin. Wannan yasa na fara tattara kaya na duk da na nemi su fadamin dalilinsu amma suka ki. Kuma duk kokarin abokan aikina su sasanta batun ya ci tura.”

“Da na bar wurin sai na sanar da kakakin rundunar ta jihar DSP Yakubu Sabo, wanda ya aiko da wani babban jami’i domin a gargade su da su kyale ni. Bayan babban jami’in ya tafi sai suka sake dawowa wai dole ne sai na bar harabar ko su tafi da ni, kuma wai zasu kwace kayan aiki na,” in ji shi.

‎Shugaban kungiyar ‘Yan Jaridun jihar Kwamrade Adamu Yusuf, ya ce suna da masaniyar abin da ya faru. Inda ya ce zasu tattauna lamarin a taron kungiyar a yau Alhamis.

 

” Zamu tattauna batun a taron mu a yau kafin mu kai maganar gaba wajen shi Kakakin ‘Yan Sandan domin sanin dalinsu na neman sai dan jaridar ya bar harabar kotun,” in  ji shi.