✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun gargadi tsageran Kuros Riba

Hukumar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta sha alwashin ci gaba da magance ayyukan tsagera a jihar. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ne…

Hukumar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta sha alwashin ci gaba da magance ayyukan tsagera a jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ne ya sanar da Aminiya haka, a zantawarsu da wakilinmu.

Ya ce “Ko kusa hukumar ’yan sanda jihar ta Kuros Riba ba za ta taba saurara wa duk wani dan ta’adda ba a fadin jihar. A kowace rana ta Allah jami’anmu suna yin artabu da ’yan kungiyar asiri, suna kama su. Don haka ba za mu taba saurara wa duk wadansu masu aikata miyagun halaye ba, ba za mu taba bari wadansu tsirarin mutane su hana mutane sakewa ba a jihar nan.”

Wannan gargadi ba zai rasa nasaba da yadda a ’yan kwanakin nan aka rika samun fadace-fadace a tsakanin kungiyoyin asiri da ba sa ga maciji da junansu a jihar ba.

Kuma an samu hatsaniya a hedkwatar Jam’iyyar PDP a Kalaba, inda aka harbi mutum biyu, daya ya mutu.

A karshe Kwamishinan ya gargadi ’yan siyas su guji amfani da matasa domin bangar siyasa.