✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun hana matasa zanga-zanga a Jigawa

Yan sanda sun tarwatsa wadansu matasan da suka shirya zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Gwamnatin Tarayya kan yawaitar kashe-kashe da…

Yan sanda sun tarwatsa wadansu matasan da suka shirya zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Gwamnatin Tarayya kan yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da fadace-fadacen kabilanci da suke faruwa a sassan kasar nan.

Lamarin ya haifar da musayar yawu a tsakanin matasan da ’yan sanda saboda abin da matasan suka kira danne hakkinsu lura da cewa sun nemi izinin ’yan sandan amma daga baya suka hana su gudanar da zanga-zangar da suka shirya za su yi a filin taro na marigayi Malam Aminu Kano.

Da yake jawabi, shugaban shirya zanga-zangar, Kwamared Umar Danjani ya nuna takaici bisa yadda ’yan sanda suka hana su gudanar da taron kasancewar ba tayar da hankalin kowa za su yi ba, inda ya ce suna so ne kawai su nuna wa duniya cewa ana fama da yunwa da talauci da rashin aikin yi a Najeriya.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta samar wa jami’an tsaro kayan aiki masu nagarta kuma wadatattu na zamani kuma ta tabbatar tana biyansu dukkan hakkokinsu domin hakan ne zai taimaka a samu zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.

Da yake jawabi, Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, Bala Senchi ya ce laifin wadanda suka shirya taron ne saboda ba su samu izinin yin taron ba saboda takardar da suka rubuta sun sanar da Kwamashinan ’Yan sanda a matsayinsa na Bala Senchi ne ba a matsayin Kwamashina ba.

Ya ce kuma ba su nemi izinin gwamnatin jihar ba saboda haka ba su da izinin su yi taro saboda wadansu za su iya amfani da wannan damar su shiga gari su afka wa dukiyar al’umma.

Shi ma da yake jawabi, Kakakin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Bello Zaki ya ce Gwamnatin Jihar ba ta da masaniya a kan hana taron.

Bello Zaki ya ce a Jihar Jigawa babu batun rashin zaman lafiya kuma batun da ake cewa wai Gwamna ne ya hana su yin zanga-zangar ba gaskiya ba ne.