✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun harba wa ‘yan majalisar Anambra barkonon tsohuwa

Hayaniya ta kaure a majalisar dokokin jihar Anambra bayan da ‘yan sanda suka harba barkonon-tsohuwa tare da rufe kofar shiga majalisar. Hayaniyar dai nada nasaba…

Hayaniya ta kaure a majalisar dokokin jihar Anambra bayan da ‘yan sanda suka harba barkonon-tsohuwa tare da rufe kofar shiga majalisar.

Hayaniyar dai nada nasaba da tsige kakakin majalisar dokokin jihar Rita Maduagwu da aka yi ranar Talata. Yayin da kakakin majalisar ya ce har yanzu yana nan akan kujerarsa, saboda ‘yan majalisar basu da hakkin tsige kakakin majalisar ko Gwamna har sai an samu kashi biyu cikin uku wadanda zasu kada kuri’a a zauren majalisar.

Maduagwu, ya kara da cewa, “har yanzu ni ne kakakin majalisar dokokin jihar”.