✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun harbe wanda ya yi garkuwa da ’yan canji ya hallaka su

Jami’an Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas sun ce sun kashe wani kasurgumin wanda ya kware wajen yin garkuwa da mutane bayan ya karbi kudin fansa…

Jami’an Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas sun ce sun kashe wani kasurgumin wanda ya kware wajen yin garkuwa da mutane bayan ya karbi kudin fansa ya kuma kashe su.

Mutumin mai suna Mufutahu Timileyin Sulaimon, wanda aka fi sani da  Pencil ya gamu da ajalinsa ne bayan barin wutar da jami’an ’yan sanda na SARS  suka yi da shi da dare ranar Lahadin da ta gabata a yankin Ikorodu da ke fama da matsalar ’yan kungiyar asiri.

Mufutahu shi ne ya jagoranci  garkuwa da wadansu ’yan kasuwar canji biyu a Legas a watannin baya inda suka kashe su bayan sun karbi kudin fansa, lamarin da ya sanya rundunar ’yan sandan ta kama mutum uku daga cikinsu inda ta yi shelar neman Pencil ruwa a jallo.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, jami’an rundunar biyu sun jikkata a lokacin da suka yi musayar wuta da jagoran masu garkuwa da mutanen.

“Kashe shi da jami’anmu suka yi nasara ce a kokarin da rundunar ’yan sandan ke yi wajen magance masu garkuwa da mutane, a yanzu mun yi maganin miyagun laifuffukan da yake jagoranta wadanda suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma aika-aikar ’yan kungiyar asiri,” inji shi.

Haka zalika,  rundunar ’yan sandan ta gano gawar wani mutum mai shekara 56  da ta farkarsa a ranar Alhamis din makon jiya a yankin Iba, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa matar mutumin ce ta shaida wa ’yan sandan cewa, an samu gawar mijinta Rasaki Balogun da ta wadda ake zargin farkarsa ce a yashe cikin jini a wani gida da yake zaune shi kadai ba tare da iyalansa ba. “Ko da jami’anmu suka isa gidan sun iske gawar mutumin da ta farkar tasa cikin jini inda aka iske gawar farkar tasa a kan wuka. Yana zaune ne shi kadai a gidan, yayin da iyalansa ke zaune a wani gida na daban, zuwa yanzu ba a gano daga ina farkar tasa ta fito ba, kuma ba a kai ga sanin ko wacece ba, don haka ana ci gaba da bincike domin gano musababbin mutuwarsu,” inji shi.