✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama barayin shanu da kwato shanu 36 a Zamfara

Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Kebbi, Garba Danjuma, ya ce rundunar ’Yan sandan jihar tayi nasarar kama barayin shanu tare da kwato shanu guda 36…

Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Kebbi, Garba Danjuma, ya ce rundunar ’Yan sandan jihar tayi nasarar kama barayin shanu tare da kwato shanu guda 36 daga hannun barayin a jihar Zamfara.

An yi nasarar kama barayin tare da kwato shanu a yankunan Zamfara da jihar Kebbi, sun samu nasarar ne lokacin da wasu mazauna kauyen Asarara su biyu Abubakar Juli da Alhaji Ardo, suka sanarwa jami’an ‘yan sandan bacewar shanun su 43.

Kwamishinan ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Birnin Kebbi, inda ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin barayin tare da shanun, yayin da wasu suka tsere.

Ya ce, sun yi nasarar kama wasu mutane guda biyu, Abubakar Umar da Attahiru Sani, mazauna garin Daki Takwas a karamar hukumar Gumi ta jihar Zamfara.

Ya kara da cewa, rundunar tana iya bakin kokarinta don ganin ta kama sauran barayin, inda ya kuma bayyana cewa suna aiki tukuru don ganin an kawo karshen sace-sacen shanu a yankunan jihar.