✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama barayin shanu da masu garkuwa da mutane a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da hadin gwiwar Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyati Allah ta kama barayin shanu uku, ta kuma gano shanun sata…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da hadin gwiwar Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyati Allah ta kama barayin shanu uku, ta kuma gano shanun sata sama da dubu daya a dajin Falgore a jihar Kano.

A jiya Alhamis Kwamishinan ‘yan sandan Kano Ahmad Iliyasu, ne ya shaida haka a lokacin da yake gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin.

Masu garkuwan da aka kama

Sa’idu Abdullahi, daya daga cikin wadanda ake zargin ya shaida wa manema labarai cewa, su ne suka yi garkuwa da wani babban mutum a kwanakin baya inda suka karbi kudin fansa Naira miliyan 10, ya ce Naira dubu 500 aka ba shi a matsayin kason sa, ya ce su biyar ne suka aikata wannan aikin inda suka yi amfani da bindigar AK47 guda biyu da karamar bindigar fistil guda, ya ce da kayan sarki na soji suke amfani wadanda mai gidan su ke karbo su daga wajan wasu sojoji inda ya kan mayar masu da kayan da zarar sun kammala aikin su na garkuwa da mutane.

Ragowar mutum biyun da ake zargi da satar shanu sun hadar da Sulaiman Abdullahi da Lawal Muhammad, wadanda suka bayyana cewa su barayin shanu ne amma basa satar mutane, suka ce iyayen gidan su na Rigacikum a jihar Kaduna wadanda idan sun saci shanun su suke kai wa, sun kuma bayyana cewa sun shafe sama da shekaru uku su na satar shanu.

Shanun da aka gano.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmad Iliyasu, ya shaida wa ‘yan jaridu cewa kwanaki 7 jami’an ‘yan sandan suka shafe a dajin Falgore tare da hadin gwiwar kungiyar fulani makiyaya ta Miyyati Allah inda suka yi bata kashi da wadanda ake zargin kafin su ci karfin su su kame su, ya ce sun gano shanu sama da dubu daya na jama’a da barayin shanu suka sace ya ce, da taimakon gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje za a tantance masu su aba kowa kayan sa.

A karshe ya jinjinawa al’ummar jihar da suke bai wa rundunar ‘yan sandan hadin kai a aikin su na kawar da batagari, ya ce ko kadan jihar Kano ba zata zamo mafaka ga batagari ba.

Wasu kayan da aka kwato