✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama Halifan Tijjaniya a Ogun bisa zargin Damfara

‘Yan sanda daga jihar Edo suka shiga jihar Ogun su kayi awon gaba da Halifan darikar Tijjaniya na jihar Malam Adamu Balarabe tare da wata…

‘Yan sanda daga jihar Edo suka shiga jihar Ogun su kayi awon gaba da Halifan darikar Tijjaniya na jihar Malam Adamu Balarabe tare da wata matar aure bisa zarginsu da hannu a badakalar damfarar da wata budurwa ta yiwa saurayinta wanda suka hadu ta kafar sada zumunta ta Facebook.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun shaida wa Aminiya cewa budurwar ta nemi taimakon Halifan Tijjaniyar ne bayan da ta damfari saurayin nata zunzurutun kudi naira miliyan biyu.

Majiyar ta ce budurwar ta hadu da saurayin, wanda mai sana’ar canjin kudi ne mazaunin jihar Edo, inda ta bukaci ya bata “Naira 20,000, amma sai ya yi kuskure ya tura mata miliyan biyu”.

Bayan ya gano kuskuren da ya yi ne sai ya “kara mata 10,000 inda ya nemi ta mayarmasa 1,700,00 amma sai ta kekashe kasa taki, ta nemi taimakon wata matar aure wacce ta kai ta wajen Halifan Tijjaniyan domin ya bata taimakon da za a karkatar da hankalin mutumin daga maganar kudin”.

Bayanai sun ce ewa Malam Balarabe ya amince yayi aikin inda aka ya nemi a ba shi 500,000, kuma aka ba shi, sannan aka baiwa matar auren da tayi hanyar malamin 200, 000.

Sai dai aikin da Halifan Tijjaniyan ya yi bai cimma manufa ba, domin mutumin ya shigar da kara ofishin rundunar ‘yan sandan jihar Edo wadanda suka yi awan gaba da wadanda ake zargin tare da budurwar.

Aminiya ta zanta da Malam Kabiru wanda kani ne ga wanda ake zargin wato Halifan Tijjaniya na Jihar Ogun inda ya shaida cewa yarinyar da ake zargi da damfarar saurayinta ta je wajen Halifan ne da zummar yayi mata aiki a zuwan ita matar aure ce ba budurwa ba.

Ya ce ta shaida masa cewa “mijinta ne mutumin kuma yana da wasu mata uku, yana kuma zalintar ta dan haka take so ta karbi kudi a hannunsa, a haka ne Halifa ya yarda yayi mata aikin domin ya taimaka mata”.

Ya tabbatar da cewa “yau kusan kwana uku ana tsare da su a can jihar Edo, amma muna sa ran za a sako su ko yau ko gobe, domin an yi yarjejeniyar cewa zai dawo da kudin da ya karba” in ji shi.

Aminiya ta tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo CP Lawan Tanko Jimeta wanda ya ce wadanda ake zargin su hudu ne “kuma dukkansu sun amsa laifinsu”.

Ya ce “a binciken da nayi matsalar ba daga yarinyar ba ce domin ita ba ta da asusun ajiya a banki na dan uwanta ta bayar ko da aka sami kuskure wajen zuba kudi ta bukaci kanin nata ya mayar da kudin sai yace a’a, ai ba haka ake yi ba, Allah ne ya tsaga da rabon ta.

“Sai shi kanin nata ya dauki miliyan daya a kudin suka baiwa malamin 500,000, sai kawarta da aka ba naira 200, 000 ita kuma ta tashi da 300, 000,” in ji CP Lawan.

Yace zuwa yanzu sun fara biyan kudin inda suka dawo da sama da naira miliyan guda.