✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama harsasai dubu 34 da aka shigo da su daga Togo

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama harsasai dubu 34 da aka shigo da su daga kasar Togo ta kan iyakar Najeriya da ke Jihar…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama harsasai dubu 34 da aka shigo da su daga kasar Togo ta kan iyakar Najeriya da ke Jihar Ogun inda wadanda ake zargin suka yi yunkurin kai su garin Anacha a Jihar Anambra.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Alhaji Ahmad Iliyasu ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan sanda  a karkashin jagorancin ACP Shattima Muhammed wadanda ke yin aikin sintiri na musanmman a kan iyakar kasar nan da ke Imeko Afon a Jihar Ogun suka tsayar da motar da ke dauke da harsasan mai lambar Legas, KSF 254 DD domin bincike, inda masu motar suka yi musu tayin ba su na goro domin su kyale su su tafi abin da ’yan sandan suka ki amincewa.

“Sun bincika inda suka samu tarin harsasai  dubu 34 da 865 da aka shirya su a cikin kwalaye aka jera su a motar, mun kuma yi nasarar kama mutum uku da suka yi wa motar rakiya, daya daga cikinsu dan kasar Togo ne mai suna Isa Muhammad ragowar biyun ’yan Najeriya ne wadanda suka hada da Alabi Fayemi da Seyi Bamgbose, za mu ci gaba da gudanar da bincike mu kamo ragowar masu hannu a lamarin. Rundunarmu ba za ta saurara ba, za mu ci gaba da dakile ayyukan miyagu,” inji shi. Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Daya daga cikin wadanda ake zargin Isa Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa wani mutum ne dan Najeriya da ke zaune garin Anacha kuma yake zuwa kasar Togo, yana sayen kwance kaya da suka hada da kayayyakin sawa da motoci ya kawo Najeriya ya mallaki harsasan.

Ya ce “Shi ne ya kira ni ya ce in zo in tuka masa motar in kai ta garin Anacha a Jihar Anambra, a lokacin da na dauko ta ba ni da masaniyar akwai kaya a cikinta, kuma ko da ya nemi in yi masa aikin sai na fada masa ba ni da lasisin tuki, amma ina da aboki dan Nigeriya wanda yana da shi zan kira shi mu yi aikin tare, ko da na kira shi na shaida masa shi ma sai ya zo da abokinsa, ya tuko motar muka shigo ta mu uku.”

“Ko da muka iso Jihar Ogun sai muka shiga garin Abeokuta muka yi gyaran kafafun motar daga nan muna yunkurin tafiya Jihar Anambara ’yan sanda suka kama mu,” inji shi.

Ya ce wanda ya ba shi motar yana fada masa idan ya je Anacha ya kira shi ta waya, ya ce lokacin da ’yan sanda suka kama su ya kira mai kayan ya hada shi da ’yan sanda suka yi magana.