Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

’Yan sanda sun kama harsasan da aka boye a cikin garin kwaki a Legas

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama harsasai 50 masu girman milimita 38 kowannensu, a wata tashar mota a Unguwar Satellite a Legas.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa jami’ansu sun samu bayanan sirri game da harsasan da aka boye a buhun garin kwaki sai suka dirfafi tashar motar inda ake kokarin yin safarar su zuwa garin Anacha, “Mun yi nasarar kama matar da ke dauke da kayan wacce ta ce wani mutum ne ya ba ta ta kai masa garin Anacha, yanzu haka ana tsare da ita ana binciken muhimman bayanai daga gare ta,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Haka zalika rundunar ‘yan sandan ta kama wadansu mutum biyu da ake zargi da kashe mai gidan da suke haya, tare da jefa shi a rijiya suka arce da motarsa kirar Toyota Camry.  DSP Bala Elkana ya ce jami’ansu sun kama wadanda ake zargin wadanda suka hada da Daniel Isaac mai shekara 38 da Emmanuel Chukwu dan shekara 36,. “Ganin yanayin da suke tuki ne jami’anmu suka yi zargin akwai wani abu a boye, nan da nan suka tare su inda suka fara bincike wanda ya nuna sun kashe mai gidan da suke haya mai suna Don Abel mai shekaru 50 suka jefa gawarsa a rijiyar gidan da ke Unguwar Owodun a Ikotun, an yi nasarar kama su ne a lokacin da suke kokarin kai motar inda za su sayar da ita,” inji shi.

Haka zalika rundunar ta kama wani dan kasuwa da ake zargin dan luwadi ne mai suna Friday Okeke, inda aka zarge shi da yin lalata da yara maza biyu masu shekara 12 da 9. Iyayen  yaran ne suka yi karar dan kasuwar bayan ya yaudari yaran ya shigar da su rumfarsa ya yi lalata da su. DSP Bala Elkana ya ce an garzaya da yaran asibiti domin bincikar lafiyarsu tare da zurfafa bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin domin ya fuskanci shari’a.

ADVERTISEMENT