✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama jami’an NDLEA na bogi a Kano

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama mutane hudu wadanda suke amfani da sunan cewa su jami’an Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun…

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama mutane hudu wadanda suke amfani da sunan cewa su jami’an Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ne.

Kakakin hukumar ‘yan sandan SP Magaji Musa Majiya ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai, ya kuma ce jami’an bogin sun dade su na karbar kudade daga hannun masu safarar kwayoyi a birnin Kano da kewaye.

Majiya ya sanar da sunayen wadanda ake zargin kamar haka: Tijjani Usman, wanda aka fi sani da O/C SARS na rukunin gidajen Kurna Kano da Muhammed Musa Haruna, wanda aka fi sani da Mo a rukunin gidaje na Darmanawa da Adamu Usman na rukunin gidaje na Brigade da kuma Uzairu Bala daga karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.