✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama ma’aikacin zabe na bogi a rumfar zabe

Jami’an ‘yan sanda na rumfar zabe mai lamba ta 017 da ke rukunin gidajen Efab a lardin Mbora na unguwar Life camp Abuja sun kama…

Jami’an ‘yan sanda na rumfar zabe mai lamba ta 017 da ke rukunin gidajen Efab a lardin Mbora na unguwar Life camp Abuja sun kama ma’aikacin hukumar zabe INEC na bogi a rumfar.

An dai kama ma’aikacin bogin ne da ya nuna yana da mukamin `Polling Officer (PO)` a rumfar zaben lokacin ake zaben ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli a babban birnin tarayya a yau Asabar.

A yayin da wakilin Kamfanin Dillanci Labarai NAN ya tattauna da jami’in dan sandan rumfar zaben DSP Mohammed Bako, ya ce sun binciki jakar ma’aikacin bogin da ya dauka amma babu wata shaida zata nuna shi ma’aikacin hukumar INEC ne.

Bayan ‘yan sanda sun tilasta masa ya bude jakar da ya kulle da makulli, sun samu wayoyin sadarwa da tufafinsa sai kuma tabarma a ciki.