✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama makiyaya 3 da ake zargi da kashe manomi a Ogun

Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun ta kame wasu Fulani makiyaya uku da ake zargi da kashe wani mutum mai suna Rafiu Sowemimo, a kauyen Alabata…

Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun ta kame wasu Fulani makiyaya uku da ake zargi da kashe wani mutum mai suna Rafiu Sowemimo, a kauyen Alabata a jihar Ogun.

Mai magana da yawun Hukumar’yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa Hukumar ta kame fulani makiyayan wadanda suka hadar da Muhammed Adamu da Saliu Ismail sai Saliu Adamu, ya ce gardama ce ta kaure a tsakanin su da manomin a lokacin da suka shiga gonar da dabobbin su inda ya yi masu magana sai suka sassare shi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar manomin mai shekaru arba’in