✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama masu garkuwa 16 a Kogi

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta kama wadanda ake zargin masu yin garkuwa da jama’a 16 ne, masu shekaru daga 16 zuwa 45 a…

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta kama wadanda ake zargin masu yin garkuwa da jama’a 16 ne, masu shekaru daga 16 zuwa 45 a Ankpa dake jhar Kogi wadanda suka shahara a fannin kisan jama’a da cire sassan jikinsu.

Kakakin hukumar ‘yan sandan Jimoh Moshood, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, wadanda ake zargin sun hada da: Yakubu Hamidu (shugaban tawagar), Abdullahi Ibrahim, Shaibu Adamu da Ubile Attah.

Sai kuma sauran: Julius Hassan, Shehu Haliru, Abdullahi Tijjani, Sale Adama, Musa Abdullahi, Yakubu Yahaya, Adama Shagari, Isaac Alfa, Baba Isah, Idoko Benjamin, Akwu Audu da Abdullahi Zakari.

Kakakin ya ce, an samu bindigogi kirar gida biyu da wasu gajerun gatarai biyu aka samu a hannunsu. Cikin wadanda aka kaman Ubile Attah da laifin yin garkuwa da jama’a shi ne ake zargi da kisan Insfekta Abdul Alfa a ranar 28 ga Nuwamba 2017.