Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 93

Hedkwatar hukumar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da nasarar kama mutum 93 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa, wadanda suka addabi jama’a a garuruwan jihohin Arewacin Najeriya.

Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda kuma kakakin hedkwatar ‘yan sandan Frank Mba, ne ya sanar da hakan a jiya bayan an kama mutanen a kauyukan Katari da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja. Kuma ya ce kama wadannan mutanen babban nasara ce da  ‘yan sanda suka yi wajen dakatar da yin garkuwa da mutane da ake yi a shiyyoyin kasar nan.

ADVERTISEMENT