✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane da ‘Yan fashi a Kaduna

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da masu sayar shanu, mutum 45 ta kuma kwato makamai da…

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da masu sayar shanu, mutum 45 ta kuma kwato makamai da harsasai a hannun wadanda ake zargin.

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Ali Aji Janga, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai ya ce, an samu nasarar ne a sakamakon kokarin rundunar na yakar masu aikata miyagun laifuka a jihar.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka kama sun bayyana cewa, su ne suka kama shaikh Algarkawi a shekarar 2018 da kashe wasu ‘Yan Sanda uku tare. Akwai kuma wadanda suka sace daliban jami’ar ABU Zariya da kuma dan Majalisar jihar Suleiman Dabo.

Kwamishinan ya kara da cewa, rundunar ta yi nasarar kwato bindigogi shida kirar Ak47 da kirar O6 daya da kananan bindiga uku da kirar hannu uku da harsasai 135 sai motoci hudu da keke NAPEP daya da sauran kayayyaki.