Aminiya

‘Yan sanda sun kama masu yi wa yara fyade uku cikin kwana uku a Legas

Matsalar yi wa yara kanana fyade tana kara kaimi duk da kokorin da jami’an tsaro da kungiyoyin ci gaban al’umma ke yi  kan lamarin.

A karshen watan jiya Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama mutum uku cikin kwana uku wadanda ake zargi da yi wa yara kanana fyade ciki har da ’yar shekara uku da ake zargin wani tsoho mai shekara 50 ya yi wa fyade.

ADVERTISEMENT

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar 30 ga Agustan da ya gabata jami’ansu sun samu labarin wani mutum mai suna Isaac Ubogu da ke zaune a Unguwar Awoniyi Elemo a Rukunin Gidaje na Ajawo ya yi wa yarinya mai shekara uku fyade. Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskaci hukunci yayin da aka kai yarinyar asibiti don kula da lafiyarta.

Ya ce a ranar 31 ga Agusta, rundunar ta kama wani matashi mai shekara 28 mai suna Fatai Nafi’u a yankin Bariga wanda shi ma ake zargi da yi wa yarinya ’yar shekara 15  fyade. DSP Bala ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a kotu a daidai lokacin da ake kula da yarinyar a asibiti. Ya ce sannan a ranar 27 ga Agusta rundunar ta kama Taiwo Sheuases, bisa zargin fyade ga yarinya mai shekara 15 a yankin Bariga. Ya ce an garzaya da yarinyar asibiti yayin da za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu domin ya fuskanci hukunci.

ADVERTISEMENT

DSP Bala ya kuma shaida wa Aminiya cewa, a ranar 30 ga Augusta rundunar ta samun labarin wani mutum mai shekara 37 mai suna Seyi Onayemi, da ake zargin ya sha guba ya hallaka kansa a yankin Ikorodu, inda aka samu gawarsa a Unguwar Odogunyan da ke kan hanyar Shagamu.