✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama matashin da ya babbake budurwarsa da wuta

Wani matashi dan kimanin shekara 19 mai suna Orji Ifeanyichukwu Victor, ya shiga komar ‘yan sandan Legas bayan da ya babbake budurwarsa Alabi Tolani Mariam…

Wani matashi dan kimanin shekara 19 mai suna Orji Ifeanyichukwu Victor, ya shiga komar ‘yan sandan Legas bayan da ya babbake budurwarsa Alabi Tolani Mariam mai shekaru 24 bisa dalilin zargin ta da neman maza.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa, matashin da ake zargin dan yahoo ne wato dan danfara ne a yanar gizo, ya kuma kama hayar gidan da yake ciki da yarinyar ne akan Naira dubu 600 da kudin damfara.

Ya ce, bayan ya hadu da budurwar ta sa kimanin watanni 10 da suka shude ya aje ta a gidan ya kuma hana ta yawan karuwanci, ” A ranar Juma’a da ta gabata ta fita daga da nufin zuwa gaida mahaifin ta da ta dawo bayan kwana guda sai ya lura a wayar ta tayi mu’amala da wani saurayi har ta aike masa da hoton ta na tsaraici lamarin da yasanya ya babbake ta da man fetur inda ta mutu bayan an kai ta asibiti.”

DSP Bala Elkana, ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.