✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mutum 11 kan zargin dukan masu aikin hanya a Jigawa

Jami’an ’yan sanda sun kama matasa 11 da ake zargi da dukan wani ma’aikacin hanya bayan da aka samu rashin fahimta a tsakaninsu. Lamarin ya…

Jami’an ’yan sanda sun kama matasa 11 da ake zargi da dukan wani ma’aikacin hanya bayan da aka samu rashin fahimta a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a kauyen Kore da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa da ke Jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Injiniyan hanyar mai suna Aminu Yusuf ya sha duka a wajen  mutanen kauyen ne saboda sun nemi ya sauya taswirar hanya daga ainahin inda take a rubuce ta koma ta cikin garinsu, amma ya ki.

Ainihin yadda tsarin hanyar yake daga kan hanyar Auno daga bakin hanyar da ta tafi Karamar Hukumar Kafin Hausa ce, sannan za ta biyo ne ta Dumadumi Toka ta Kwarin Larabar Kuka ta wuce zuwa Majerin Zangoma sannan ta bulle zuwa Majeri Gari ta gangara zuwa Dumadumi Kyaure ta nufi Balago.

Matasan da suka ga garinsu an bar shi a gefe, hakan ne ya sa suka dauki doka a hannu suka yi wa Injiniya Aminu duka da sauran abokan aikinsa da suka hada da Bashir Wakili da Salisu da Haruna Monday.

’Yan sanda sun kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne mai suna Salisu Yusuf mai shekara 24, wanda ya bayyana wadansu matasa 10 wadanda ya ce tare suka yi dukan. Kuma ’yan sanda sun kama babura uku da suka yi amfani da su domin zuwa wajen da sanduna da gatari da sauransu.

SP Audu Jiniiri ya ce, da zarar sun kammala bincike a kan wadanda suke tuhumar za su gurfanar da su a gaban alkali domin su fuskanci hukunci.