✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama mutum 40 da miyagun makamai a Kebbi

Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta samu nasarar kama mutum 40 da miyagun makamai a yayin gudanar da zabubbukan fid da gwani da suka gudana…

Hukumar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta samu nasarar kama mutum 40 da miyagun makamai a yayin gudanar da zabubbukan fid da gwani da suka gudana a fadin jihar. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ibrahim M Kabiru lokacin yake zantawa da manema labarai a ofishinsa a Birnin Kebbi.

Kwamishinan ya ce “Muna gudanar da bincike kan yadda ’yan bangar siyasar ke samun miyagun makaman da wadanda suke daukar nauyinsu. Idan muka gane ko su wane ne za mu kame su mu gabatar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.”

Ya ce “Duk wanda ya zo da sunan karbar beli za a kai shi kotu domin shi ma a yi masa hukunci kan goyon bayan mai laifi. Wadannan da ake zargi an kama su ne a kananan hukumomin Birnin Kebbi da Bunza da Kamba da Bagudo dauke da makamai suna cin zarafin masu kada kuri’a.

Ya ce hukumar ’yan sandan ta kira taron shugabannin jam’iyyun siyasa ta bayyana musu irin makaman da aka haramta amfani da su a yayin gudanar da zaben fid da gwani da kuma lokacin yakin neman zabe a  Jihar Kebbi.

“Kuma dukan shugabannin jam’iyyun sun amince za su tabbatar da cewa magoya bayansu sun bi dokar. To amma bayan kammala taron sun sanya hannu da kuma daukar alkawarin cewa ba za su amince da duk wani mai goyon bayan jam’iyyarsu ko dan banga ya karya dokar da ’yan sanda suka gindaya ba,” inji shi.

A cewarsa sai ga shi rundunar ta cafke wadansu ’yan bangar siyasa na jam’iyyun daban-daban dauke da miyagun makamai da ta haramta amfani da su.

Ya yi kira ga jama’a su ci gaba da taimakawa da bayanan sirri ga rundunarsa domin ta iya dakile duk wani laifi da ake aikatawa a cikin jihar. Ya kara kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa a jihar su dada sanya ido  don ganin sun hana magoya bayansu daukar miyagun makamai yayin gudanar zabe ko bayan kammala zabubbuka a jihar.

Ya ce ’yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin ganin sun tabbatar da an gudanar da zabe a jihar da kuma kasa baki daya cikin kwanciyar hankali da lumana ba. Daga nan ya ce “Wannan umarni ne daga shugaban ’yan sanda na kasa ga dukan kwamishinonin ’yan sanda na  jihohin kasar nan.

A karshe Ibrahim M. Kabiru ya ce da zarar jami’ansa suka kammala bincike za a gabatar da wadanda ake zargi da laifin a gaban kotu kan zargin daukar miyagun makamai yayin gudanar da zabe da kuma tayar da tarzoma lokacin zabe.