Aminiya

‘Yan sanda sun kama mutum 57 kan zargin aikata miyagun laifuffuka a Jihar Oyo

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama mutum 57 da ake zarginsu da aikata miyagun ayyuka daban daban a jihar.  Daga cikinsu 43 daga ana zarginsu da aikata fashi da makami ne yayin da aka kama daliban Jami’ar Ekiti 4 kan zargin shiga cikin kungiyar asiri ta AIYE, inda aka same su da rigunan singileti da huluna hana-salla masu dauke da tambarin kungiyar. Haka kuma an nuna wadansu matasa 4 ’yan wata kungiyar asiri ta daban da ake zargin suna tsafe-tsafe da tayar da hankalin jama’a a birnin Ibadan.

Da yake nuna mutanen a wani taro da ’yan jarida a ofishinsa a ranar Juma’a da ta gabata Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu wanda ya nuna wadansu mutum biyu da aka kama su bisa zargin mallakar kokon kawunan mutum biyu. Kuma ya sake nuna wani mai gadin wata makaranta mai shekara 50 mai suna Tajudeen Olalere da ake zargi da yi wa daliban makarantar fyade a lokuta daban-daban a baya. Akwai kum mutum daya mai suna Ahmed Musa da aka kama a garin Eruwa kan zarginsa da satar wata matar aure mai suna Foluke Akinrinde da jami’an yaki da masu satar mutane a Jihar Oyo suka kubutar da ita tare da kama mai wanda ake zargin.

ADVERTISEMENT

Kwamishina Shina Olukolu ya ce an kama mutum 11 dukkansu maza masu shekara daga 21 zuwa 44 da ake zargin sun kware wajen yin fashin manyan motocin tanka masu dauke da man fetur ta amfani da bindigogi domin tsoratarwa zuwa maboyarsu. Ya ce ’yan sanda masu yaki da fashi da makami (SARS) a jihar ne suka kama mutanen.

Wani gungun ’yan fashi da makami su biyar an kama su ne da kan zargin satar sababbin tayoyin tirela guda 20 da durom 2 na bakin mai da sababbin baturan tirela mallakar Kamfanin Ocean da ke Moniya a garin Ibadan.

ADVERTISEMENT
Wadansu matasa da ake zargi da aikata laifuffuka

Dukkan mutanen da aka kama ba su musanta miyagun ayyukan da ake zargin sun aikata ba yayin gabatar da su. Kuma a yayin da Kwamishinan yake nuna su ga ’yan jarida, ya nuna bindigogi da adduna da wukake da kayan tsafi da kananan motoci 4 da wayoyin salula da na’urorin kwamfuta da aka samu a wurinsu. Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da mutane a gaban kotu don hukunta su daidai da irin laifin da suka aikata.