✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama mutum biyu da shanun sata 26 a Jihar Oyo

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wadansu matasan Fulani biyu da  aka same su da shanu 26 da ake zargin sun sato su ne…

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wadansu matasan Fulani biyu da  aka same su da shanu 26 da ake zargin sun sato su ne daga makwabciyar jihar don sayarwa ga barayin zaune. Matasan masu suna Muhammadu Usman da Alhaji Majo suna daga cikin mutum 45 da aka kama bisaa zargin aikata miyagun ayyuka  a sassan jihar.

Da yake nuna mutanen da makaman da aka samu tare da su a wajen taro da ’yan jarida a Ibadan Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Shina Olukolu ya ce labarin sirri da suka samu ne ya kai ga kama ’yan fashin shanu su biyu da abokansu da suka tsere. Ya ce an kama su ne a dajin Akinmorin a kusa da garin Oyo. Kwamishina Olukolu ya ce za a mayar da shanun ga ainihin mutanen da suka mallake su bayan kammala bincike.

A zantawa da Aminiya Muhammadu Usman ya ce “A gaskiya mun tarar da wadannan shanu ne a cikin wata fadama suna kiwo ba tare da makiyayi ba sai muka koro su muka taho da su zuwa wannan wuri domin sayarwa. Babu bindiga ko adda a tare da mu lokacin da muka koro shanun inda kaddara ta rutsa da mu aka kama mu.”

Shi kuwa Alhaji Majo cewa ya yi “Duk abin da ka ji wannan ya fada maka ni ma haka zancen yake sai dai karin bayani shi ne mun aikata haka ne saboda babu komai a tare da mu kuma Allah ne Ya jarabce mu. Wannan ne karo na farko da muka yi satar shanu kuma mun yi takaicin aikata hakan muna so ka gaya wa gwamnati ta yi hakuri ta yafe mana.”

Kwamishina Shina Olukolu wanda yake tare da Mataimakinsa Attahiru Isa ya nuna wani mutum mai suna Sadik Abiodun da ake zargi ya saba sanya kayan soja yana sojan-gona inda yake yi wa mata fyade da kwace kudin mutane.

Asirin Sadik ya tonu ne a lokacin da jami’an tsaro  na SARS suka kama shi a maboyarsa da ke Papa Eleye a Olomi da ke Ibadan jim kadan bayan yi wa wata mata mai suna Alimot Isma’il fyade.

Cikin mutanen da aka nuna akwai mutum biyu masu suna Staley Ezenna da Rotimi Afolabi da ake zarginsu da amfani da makami wajen kwace mota kirar Toyota Camry da tsabar kudi Naira miliyan biyu daga hannun wani mai suna Tunde Omilana a gidansa da ke Amama a garin Ogbomoso. Sauran mutanen da aka nuna sun hada da wadanda ake zargi da garkuwa da mutane da  fashi da makami da damfara wadanda aka same su da makaman da suke amfani da su wajen aikata ayyukansu.

Kwamishinan ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da dukkan mutanen a gaban kotu domin hukunta su.