Aminiya

’Yan sanda sun kama sojoji biyu kan fashi da makami

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta kama sojoji biyu bisa zargi aikata laifin fashi da makami.

Kakakin Rundunar, DSP Sulaiman Nguroje ne ya bayyana haka, inda ya ce an kama sojojin ne da misalin karfi 1:00 na dare a hanyar da aka fi sani da Target Junction a tsakiyar garin Jalingo yayin da suke kokarin gudu.

ADVERTISEMENT

Ya ce ya kamata a ce sojojin suna bakin aikinsu ne a can Karamar Hukumar Munguno da ke Jihar Borno inda aka tura su yaki da Boko Haram amma sai ga shi an kama su suna kokarin kwace wa wata mace mota ta hanyar amfani da bindiga.

“Sojojin da ake zarginsu da fashin sun sanya wa wata mace bindiga a kai inda suka tilasta ta da ta sakar musu motarta kirar Toyota Camry,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce mutanen da ke kusa ne suka yi hanzarin kai kara ofishin ’yan sanda wadanda suke sintiri, hakan ya sanya suka bi su da motarsu har suka samu damar kama su.

Kakakin ’yan sandan ya ce sun ci nasarar kama motar da bindiga kirar AK47 da ke dauke da harsasai 35.

Daya daga cikin sojojin mai suna Dampa Hyellambamun ya bayyana wa manema labarai cewa shi soja ne da ya kamata yana Karamar Hukumar Munguno a Jihar Borno.

Ya kara da cewa ya karbi izinin hutu kafin ya baro Munguno amma adadin kwanakin da aka ba shi ya kare tun 10 ga Augustan da ya gabata amma bai koma ba.

Ya bayyana wannan fashi da suka yi da cewa ba laifinsa ba ne, inda ya ce gwamnati ta ba shi bindiga amma ba ta biyansa albashinsa da wasu alkawura da ta daukar musu na kudi hakan ya sanya shi aikata wannan aika-aikar.