✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama ’Yan fashi 4 da matasa 60 a Bauchi

Hukumar ’Yan sandan jihar Bauchi ta ce, ta kama mutum hudu da ake zarginsu da aikata fashi da makami da kuma wasu matasa 60 ‘yan…

Hukumar ’Yan sandan jihar Bauchi ta ce, ta kama mutum hudu da ake zarginsu da aikata fashi da makami da kuma wasu matasa 60 ‘yan Sara-Suka a yankunan jihar. An tsare wadanda ake zargin a Hedkwatar ‘yan sandan jihar Bauchi.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar DSP Kamal Datti Abubakar ne ya sanar da hakan kuma ya ce, hakan na daga cikin kokarin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar,  Habu Sani Ahmadu ke yi wajen dakile aikata laifuka. An kama wadanda ake zargin ne ranar 2 ga watan Yuni 2019 a shirin ‘yan sanda na Operations Puff Adder wanda ke yaki da miyagun ayyuka.