Da Dumi Dumi

’Yan sanda sun kama ’yan fashi da masu fasa shaguna a Jigawa

Wasu daga cikin wadanda ake zargi
Wasu daga cikin wadanda ake zargi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta gabatar da wadansu matasa bakwai da take zargin ’yan fashi da makami ta kama da wukake da adduna da kwari da baka da bindigogin baushe a yankin Gagarawa.

Hakan zalika rundunar ta kama wadansu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano da take zargin sun kware wajen fasa shaguna suna sata da masu satar babura da sauransu.

Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Jigawa Usman Sule Gomna ya ce kasancewar jihar ta manoma ce mafiya yawan ayyukan ta’asa sun fi faruwa ne a kauyuka kuma haka ya sa suka hada karfi da kungiyoyin sa-kai da jama’ar garin don tona asirin batagari don kawo karshen ta’asar.

Ya kara da cewa sun dauki matakai masu tsauri wajen yin yaki da batagari a fadin jihar.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya kware wajen satar babura, Kabiru ya ce ya shiga satar ce saboda ’yan uwansa sun hana shi ya yi amfani da kudin gadonsa, inda suka hada baki da dagacin garinsu suka hana shi dukiyarsa.

ADVERTISEMENT

Wadanda aka kama kan zargin fasa shaguna a Karamar Hukumar Ringim, daya daga cikinsu cewa ya yi shi sana’ar fawa yake yi, kuma wadansu ne suka shigar da shi harkar sata.

Sun yi nadamar yin satar, kuma suka ce idan aka sake su ba su ba sata har abada.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya