✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama ’yan fashi da motoci masu tsada

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama ’yan fashi da makami su 12 da kananan motoci 13 masu tsada a tare da su da bindigogi…

Yan sanda a Jihar Oyo sun kama ’yan fashi da makami su 12 da kananan motoci 13 masu tsada a tare da su da bindigogi guda 3 tare da wasu na’urorin aikewa da sakonni da gwala-gwalai da wayoyin salula. Wasu daga cikin barayin sun yi bayanan irin dabarun da suka yi wajen kashe mutane da kwace motocinsu da kudade da sauran kadarori.
Da yake nuna barayin ga taron ’yan jarida a ofishinsa a Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Muhammed Abdulkadir Indabawa ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne tun daga ranar 27 ga watan jiya a lokaci da wani tsohon Janar na sojojin sama, ya ba su labarin irin barnar da ’yan fashi suka yi masa a cikin gidansa da ke Ogbomoso. Sun sace wata mota kirar Toyota Highlander da kudade da wayoyin salula da na’urorin aikawa da sako. “Daga wannan lokaci ne rundunar yaki da ’yan fashi da makami (SARS) a yankin Oyo/Ogbomoso ta fara bincikenta, wanda ya kai ga nasarar kama mutum 6 a maboyarsu, wadanda su da kansu suka yi mana bayanin yadda za a gano sauran mutum 6 da suke sayen satattun kayan daga hannunsu. Daga cikin mutum 6 masu sayen kayan satar, har da wani lauyan bogi mai suna Babatunde Oretuyi. Mun riga mun tuntubi kungiyar lauyoyi ta jihar Oyo domin samun tabbacin bayanin wannan mutumi”, inji kwamishinan.
A binciken da ’yan sanda suka gudanar sun kiyasta kudin wadannan satattun motoci gauda 13 a kan Naira miliyan 30 ne kuma barayin sukan sayar da satattun motocin ne da arhar gaske ga masu saye daga hannunsu.
Wakilinmu ya ce duka barayin su 12, an kawo su ne sanye da ankwa a hannaye da kafafu bayan an rufe musu idanu da wasu kyallaye. Mafi yawanci daga cikinsu suna dauke da raunuka a kafafu da ba sa iya yin tafiya sosai, amma dole suke takawa. Kwamishinan ’yan sanda Muhammed Indabawa ya ce wannan nasara da rundunar ta samu ya nuna irin kwarewa da hazikanci na jami’ansa ne wajen yin binciken kwakwaf da ya kai su gano maboyar barayin da kama su tare da samun wasu bayanai da za su kai ga samun nasara a nan gaba.
Ya ce da zarar sun kammala bincike za su durkusar da mutanen ne gaban kotu.