Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
‘Yan sanda sun kashe ‘yan fashi 3, sun kama biyu

‘Yan sanda sun kashe ‘yan fashi 3, sun kama biyu

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Anambra ta kashe mutum uku da ta ce ‘yan fashi ne sannan ta kama wasu biyu ranar Alhamis a Onitsa, cibiyar kasuwancin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Haruna Mohammed, ya fitar ranar Juma’a, ta ce an kashe ‘yan fashin ne bayan wata musayar wuta da aka yi da su.

“Da misalin karfe 2:00 na daren Alhamis rundunar musamman ta ‘Puff-Adder’ ta amsa wani kiran gaggawa a unguwar Federal Housing Estates Fegge da ke Onitsa,” kamar sanarwar ta bayyana.

Ta ci gaba da cewa: “Nan take ta dakile wani gungun mutum biyar da ake zargin sun hari wani mai suna Nmandi, inda suka karbe masa kudin da ba a bayyana yawansu ba. Sun bude wa ‘yan sanda wuta yayin da su ma suka mayar da wuta kuma suka kashe uku tare da kama biyu.”

SP Haruna, ya ce an kwato tsabar kudi Naira dubu 900 daga hannun su da bindigogi biyu da harsasai da zoben gwal da wayoyin hannu guda hudu. Sai dai har yanzu ba a gano daga inda suka fito ba.