Da Dumi Dumi

‘Yan sanda sun kubutar da yarinya ‘yar shekara 3 da aka sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta bada sanarwar kubutar da wata yarinya mai shekaru uku, wanda ake zargin an yi safarar ta ne daga yankin Ukpor aka kuma kubutar da ita a garin Osumeyi da ke Karamar hukumar Nnewi ta Kudu jihar Anambra.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra SP Haruna Muhammad, ne ya sanar da hakan yau ga manema labarai, inda ya bukaci duk mai bayanai game da yarinyar ya tuntubi Rundunar ‘Yan sandan a lambar wayar salula kamar haka: 08060970639.

SP Haruna Muhammad, ya ce an kubutar da yarinyar ne a jiya Talata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya