Daily Trust Aminiya - ’Yan sanda sun kwato dan Majalisar Bauchi da aka sace
Subscribe

’Yan sanda sun kwato dan Majalisar Bauchi da aka sace

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta kwato dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Lame a karamar Hukumar Toro Alhaji Yusuf C. Nuhu, bayan ya share kwana goma a hannun ’yan bindigar da suka sace shi.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mohammed Ladan ne ya bayyana haka lokacin da yake nuna dan majalisar ga manema labarai a karshen makon jiya, inda ya ce bayan samun rahoton sace dan majalisar a kauyensu Zalau a karamar Hukumar Toro ranar 3 ga Maris, ’yan sanda da ’yan banga sun bi mutanen inda a karshe a cikin daren suka bar motarsu kirar Gulf 3 a kauyen Rahama da ke kusa da Saminaka a Jihar Kaduna, suka shiga daji da dan majalisar inda ya share kwana goma tare da su.
Ya ce a ranar 13 ga Maris ne suka samu kubutar da shi lokacin da suka tare wata mota kirar Gulf 3 a kauyen Tashar Mai’allo a kusa da Rimin Zayem.
Kwamishinan ya ce sun yi dauki ba dadi da mutanen a ranar da misalin karfe 10:30 na dare kuma a sakamakon hakan hasrashi ya samu wata yarinya mai suna Hauwa Auwalu a kafa inda bayan kai ta asibiti ta rasu.
Ya ce mutanen sun gudu sun bar motoci biyu masu lambar Kano da Kaduna da harsasai da wuka da sauran kayayyaki.
Wakilinmu ya zanta da dan majalisa Yusuf C. Nuhu a hedkwatar ’yan sanda, inda ya ce a iya zamansa da na kwana 10 da wadanda suka sace shi idonsu a rufe yake kuma su hudu ne dauke da makamai.
Ya ce ya rika cin biskit da tumatir da ganyaye don ya rayu da kuma gudun rudewar ciki, “Duk tafiyar da suka yi da ni a cikin Jihar Bauchi ne zuwa Kaduna kuma yawanci da dare suke yi har zuwa lokacin da na kubuta. Ina godiya ga Allah kuma na gode wa dukkan wadanda suka taimaka mini da addu’a har na kubuta,” inji shi.
An jima ana rade-radin ganin wasu mutane dauke da makamai suna kai-komo a cikin dazukan yankin Toro da Ganjuwa da Darazo a Jihar Bauchi, kuma dan majalisar shi ne mutum na uku da aka sace a jihar da suka hada da tsohon dan majalisar wakilai Sama’ila Ilali a Darazo da kuma wani ma’aikacin allurar rigakafin cutar shan inna.

texem
More Stories