✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun mallaki gidajen kansu a Ibadan

Hukumar ’Yan Sanda ta kaddamar da bikin bude wasu rukunin sababbin gidajen zamani a Ibadan, wadanda ta gina da hadin gwiwar Bankin Gama Kai da…

Hukumar ’Yan Sanda ta kaddamar da bikin bude wasu rukunin sababbin gidajen zamani a Ibadan, wadanda ta gina da hadin gwiwar Bankin Gama Kai da Bayar da Jingina (CMB) domin amfanin kananan jami’an ’yan sanda a Jihar Oyo. Rukunin Gidajen guda dubu 1da aka rada masu sunan Shugaban ’Yan Sanda na Kasa, Ibrahim Kpotun Idris, sun hada da nau’in bene hawa daya da gidaje masu dakuna biyu zuwa uku ne.

A cikin jawabin da ya karanta a madadin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa, Ibrahim Idris, Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa Sashen Gudanarwa da Harkokin Kudi, Maigari Dikko wanda ya yanke kyallen bude rukunin gidajen tare da mika takardun mallakar gidajen ga wasu jami’ai da suka yi nasarar samun gidanjen.

Sannan kuma ya tunatar da ’yan sandan kasar nan a game da alkawarin da ya yi masu a ranar 22 ga Watan Yuni na shekarar 2016 a lokacin da ya kama ragamar mulkin, cewa zai yi iya kokarinsa don ganin an kyautata rayuwar ’yan sanda a zamaninsa. Ya ce, wannan rukunin gidaje da aka yi bikin bude wa a Ibadan suna daga cikin alkawarin da ya yi.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani a kan gina irin wadannan rukunin gidaje a jihohi 36 na kasa da Abuja, Mataimakin DIG Maigari Dikko, ya ce, “makasudin samar da wadannan gidaje shine domin a taimaka wa kananan ‘yan sanda su mallaki gidaje na kashin kansu a lokacin da suke kan aiki ko bayan sun bar aiki.”

Ya ce, “Daukar matakin gina irin wadannan gidaje da Shugaban ’Yan Sanda na Kasa, Ibrahim Idris ya yi a lokacin da ya kama ragamar jagoranci shekaru biyu da suka gabata, ya biyo bayan lura da ya yi cewa daya daga cikin matsalolin da ’yan sanda suke fuskanta a kasar nan shine rashin muhalli na kashin kansu. Dalilin kenan da yasa ya dauki matakin nemo wadanda za su gina irin wadannan gidaje a kan farashi mai sauki.”

Da yake amsa wata tambaya, Maigari Dikko cewa ya yi “farashin gidajen ya kama ne daga Naira Miliyan 5 zuwa 6 kuma kananan ‘yan sanda daga kurtu zuwa masu mukaman Sufeta ne za su ci moriyar gidajen da za su rika biya kadan-kadan daga cikin albashinsu a kowane wata.”

Mai ba Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo shawara a kan Harkokin Tsaro, Mista Femi Aboderin, wanda ya wakilci gwamnan a yayin da Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa shiyya ta 11 a Osogbo, AIG Danjuma Muhammed Ibrahim da Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Oyo, CP Abiodun Odude da mataimakansa DC Attahiru Isa da DC Buba Sanusi suka jagoranci dukkan jami’an ‘yan sanda, DPO na sassa daban-daban a Jihar Oyo zuwa wajen bikin wanda aka gudanar a kan idanun wasu sarakuna da shugabannin kungiyoyi.