✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun mika shanun sata dubu daya ga Gwamnan Kano

A jiya Lahadi Hukumar ‘yan sandan Kano ta karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu, ta mika wa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje,…

A jiya Lahadi Hukumar ‘yan sandan Kano ta karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu, ta mika wa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shanu sama da dubu daya da ta kwato daga hannun barayin shanu a dajin Falgore da kewayen sa.

Da yake mika wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, shanun Kwamishinan ‘yan sandan Ahmed Iliyasu, ya gabatar da mutum hudu da ake zargin da laifukan satar shanu da garkuwa da mutane wadanda da rundunar ta kama tare da makaman su da kayan sarki na sojin Najeriya, ya ce ko kadan jihar Kano ba zata zamo mafaka ga batagari ba, inda ya jaddada aniyarsa na ci gaba da aiki da al’ummar jihar domin samun nasarar a yaki da miyagu, ya kuma yabawa kungiyar fulani makiyaya ta Miyyati Allah reshen jihar wadanda suke taimakawa rundunar a yunkurin ta na kawar da masu garkuwa da mutane da barayin shanu a jihar.

Makaman da aka kwato

A lokacin da ake mika shanun ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa za a mika su ga gwamnatin da aka kafa wanda zai zakulo masu shanun ya tantance su ya mika masu shanun su.