✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan sanda sun rufe asibiti tare da kama likitan bogi

’Yan sandan a Jihar Adamawa sun rufe wani asibiti tare da kama likitan bogi a Unguwar Modire-Yolde Pate da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu.…

’Yan sandan a Jihar Adamawa sun rufe wani asibiti tare da kama likitan bogi a Unguwar Modire-Yolde Pate da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar, DSP Sulaiman Nguroje ne ya tabbatar da faruwar haka ga manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata.

Kakakin ya ce an kama likitan bogin mai suna Gambo Adamu wanda a halin yanzu yana tsare a gidan yari.

Ya ce Malam Gambo Adamu  yana sayar da magunguna ne ga mutane inda kuma ya shiga kwantar da marasa lafiya a asibitin.

“An kama Malam Gambo Adamu ne ranar 24 ga Oktoba sakamakon rahotanni da muka samu a kansa. Bisa binciken da muka gudanar, Gambo Adamu mai sayar da magunguna ne amma sai ya mayar da gidansa mai dakuna uku zuwa karamin asibiti inda yake ganin marasa lafiya har da kwantar da wadansu.

A halin yanzu dai mun kai shi kotu sannan yana tsare a gidan kaso har sai mun gama gudanar da bincike,” inji shi.

Kakakin ya ce tuni an kulle asibitin sannan suna kokari wajen hada kai da kungiyoyin likitoci na jihar da kasa baki daya don gudanar da cikakken binciki ta yadda za a dakile masu aikata irin wanan laifi.

DSP Nguroje ya yi kira ga jama’a su ba su hadin kai da goyon baya wajen kai karar duk wanda aka samu yana aikata irin wannan aiki.