✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun rufe otel bayan kashe wata budurwa a Sakkwato

Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ta rufe wani otel mai suna Edecutibe da ke kan Titin Kano da ke fadar jihar bayan umarnin da ta…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ta rufe wani otel mai suna Edecutibe da ke kan Titin Kano da ke fadar jihar bayan umarnin da ta samu a kotu dalilin rasuwar wata yarinya.

A taron manema labarai da Kwamishinan ’Yan sanda Ibrahim Sani Ka’oje ya yi, ya ce kotu ta ba da umarnin rufe otel din ne domin wurin ya zama matattarar batagari da aikata ayyukan da suka saba wa addini da dokokin kasa.

Rundunar ta ce ta kama wadanda take zargi kawalai ne su  biyu masu aiki a otel din kan zarginsu da hada baki wajen salwantar rayuwar yarinya da suke hulda da ita.

Ya ce wata mata Sadiya Adamu da ke Unguwar Kofar Kware ta kawo musu koken Saifullahi Aminu da Yusuf Maidamma Yaboda aka fi sani da Dumguzun cewa sun yaudari kanwarta Hadiza Adamu mai shekara 26 ta rika aikata abubuwan da ba su dace ba a otal din Edecutibe,  inda suka bai wa Abdullahi Jakolo da Shamsudden Lawal na Jihar Kano ita suka fita da ita a can ne ake zargin sun ba ta kwayoyi ta sha ta fita hayyacinta nan take aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Jihar domin nema mata magani, daga baya ta rasu.

Rundunar ta gabatar da wani barawon babur da ya kashe mai babur din da ya dauko shi, ya gudu da babur din.

Kwamishinan ’Yan sandan ya kuma gabatar da wadansu da ake zargi da aikata luwadi da wani da ake zargi da yi wa wata fyade da wasu ake zargin barayin batur na sola da sauransu.