Da Dumi Dumi

’Yan Sanda sun tabbatar da sace mutum 6 a hanyar Kaduna zuwa Abuja 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutum shida akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin din nan data gabata.

Kakakin Rundunar ‘yan Sandan Yakubu Sabo, ne ya sanar da hakan inda ya ce sun samu bayanan aukuwar lamarin daga bakin DPO na Rijana da misalin karfe 8: 30 na yamma.

Yakubu, ya ce wadanda aka sace suna tafiya ne a cikin motar bas mai lamba REG NO ABJ 905 XC kuma wadanda suka sace su suna sanye ne da kayan sojoji.

Kakakin na ‘yan Sanda ya kuma kara da cewa, tuni an tura da jami’an tsaro wadanda suka yi nasarar kubutar da wata yarinya ‘yar shekaru 17 mai Suna ‎Rofiat Tijjani da wani mutum dukkaninsu mazauna Tudun Wada.

Ya ce, dukkanin wadanda suka kubuta an kaisu ofisin ‘Yan Sanda tare da  motar da suke ciki.

ADVERTISEMENT

Rundunar ta kuma bayyana cewa suna ci gaba da neman yadda zasu kubutar da sauran wadanda aka sace.

Share