✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun budewa mabiya shi’a wuta a Abuja

Rahotanni a babban birnin tarayya Abuja na cewa ‘yan sanda sun bude wuta a kan mabiya mazhabar Shi’a masu zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh…

Rahotanni a babban birnin tarayya Abuja na cewa ‘yan sanda sun bude wuta a kan mabiya mazhabar Shi’a masu zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky yau Litinin.

Rahotan na bayyana cewa, an harbi wasu daga cikin ‘yan shi’an lokacin da ‘yan sandan suka dinga harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar a wajen da suka taru kusa da babbar Sakatariyar gwamnati.

Gidan talbijin na ChannelsTV ya ce an harbi daya daga cikin ma’aikatansu a ciki a lokacin yamutsin.

Wasu daga cikin ‘yan shi’an sun ce, ‘yan sanda ne suka bude musu wuta alhali su ba su da makamai lokacin da suke zanga-zangar.