Da Dumi Dumi

‘Yan sanda sun yi awon gaba da Shaikh Bello Yabo

Malam Bello Yabo
Jami’an ‘yan sanda sun tafi da sanannen malamin addinin Musulumci a jihar Sakkwato,  Malam Bello Yabo daga  gidansa dake unguwar low-cost da karfe 5 na yamma.
Majiyarmu ta ce ana zaton ‘yan sandan sun zo ne daga Yankin Babban Birnin Tarayya suka tafi da malamin kan wani wa’azi  da ya yi game da rufe mutane da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya yi.
A wa’azin  malamin, ya caccaki gwamna El-Rufa’i  kan tsarin matakan kulle da ya yi wa al’umar jihar Kaduna .
Iyalan Malamin sun ki su ce komai kan lamarin a lokacin da wakilin Aminiya  ya tuntube su.
A nasa bangaren, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Sakkwato Muhammad Sadik ya ce bai da wata masaniya kan lamarin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya