✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…’Yan sanda sun yi yunkurin hana Gwamnonin G-7 taro a Abuja

Jami’an tsaro da suka ce suna aiki ne ‘bisa umarni daga sama’ sun gaza hana taron gwamnonin G7 da ke rikici da uwar Jam’iyyar PDP…

Jami’an tsaro da suka ce suna aiki ne ‘bisa umarni daga sama’ sun gaza hana taron gwamnonin G7 da ke rikici da uwar Jam’iyyar PDP da ya gudana a masaukin baki na Gwamnan Kano da ke unguwar Asokoro da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.

Gwamnonin da suka hada da Mu’azu Babangida Aliyu da Rabi’u Musa Kwanwaso da Sule Lamido da Rotimi Amaechi da Murtala Nyako da wasu manyan shugabannin sabuwar PDP ciki har da shugabanta Alhaji Abubakar Kawu Baraje na cikin wadanda suka halarci taron.
Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ana fara taron da misalin karfe 7:00 na yamma, sai manyan motocin hudu shake da ’yan sanda a karkashin DPO din Asokoro CSP Nnanna Amah suka iso suka nemi shiga harabar gidan, amma sai jami’an tsaron gwamnonin biyar suka hana su.
Da hatsaniya ta kaure kan hana su shiga ne gwamnonin suka ji sai suka fito don ganin abin da ke gudana inda suka gayyaci jagoran ’yan sanda ciki don bayyana musu abin da ya kawo su, inda shi kuma ya shaida musu cewa ya samu umarni daga sama cewa su dakatar da taron ko kuma a kama su.
An ce gwamnonin sun shaida masa cewa tsarin mulki ya ba su damar su taru, amma in yana ganin ba haka ba ne ya kama su. Sai DPO din ya yi turus jimawa kadan ya fice ya bar jami’ansa taron ya ci gaba da gudana.
Gwamna Kwankwaso wanda ya yi magana da manema labaraia karshen taron ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce DPO din ya shaida musu cewa ya samu umarni daga Fadar Shugaban kasa kan ya hana taron ko ya kama su. Gwamna Kwankwaso wanda ya ce wannan ba cin zarafin su ba ne kawai cin zarafin al’ummar jihohinsu ne da suke wakilta. Ya ce, “Ko a zamanin mulkin soja ba su ga irin wannan kama-karya ba, don haka abin takaici ne hakan ya auku a lokacin dimokuradiyya da kowane mutum ke da ’yancin bayyana ra’ayi ko shiga kungiya.”
Ba a samu jin tab akin Kakakin ’yan sandan Abuja Hyelhira Altine Daniel ba, lokacin hada rahoton saboda layukan wayoyinta sun ki tafiya.
Kakakin sabuwar PDP Eze Chukwuemeka Eze ya la’anci lamarin inda ya ce jiga-jigan sabuwar PDP na taro don duba ci gaban da aka samu da karbar rahotannin kwamitoci tare da daukar mataki na gaba na kungiyar ne sai ’yan sandan suka auka musu, suka nemi a dakatar da taron ko su yi amfani da karfi, inda jagoransu CSP Amah ya ce ya samu umarnin haka ne daga Fadar Shugaban kasa.