✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda za su hada kai da mutanen gari wajen kakkabe miyagu a Kano

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Malam Habu Ahmad Sani ya ce rundunarsu za ta inganta alakarta da mutanen gari wajen ganin an kakkabe aikata…

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Malam Habu Ahmad Sani ya ce rundunarsu za ta inganta alakarta da mutanen gari wajen ganin an kakkabe aikata laifuffuka a fadin jihar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko a Kano.

Habu Sani ya ce rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin sa-kai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewarsa, rundunarsu za ta tabbatar da cewa, “Bangaren kyautata alaka tsakanin ’yan sanda da jama’ar gari zai kara kaimi wajen tabatar wa jama’a damar ganawa da mu kai-tsaye ta hanyoyi da muka tsara. Tuni muka umarci shugabbannin ofisoshin ’yan sanda da ke sassan jihar su tabbatar cewa a kowane mataki an kyautata wannan dangantaka domin samo hanyoyin magance matsalar tsaro a jihar nan.”

Kwamishinan ya gargadi masu aikata laifuffuka su tuba domin ’yan sanda ba za su zuba musu idanu ba.

Kwamishina Habu Sani ya kama aiki ne a matsayin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ne a ranar 20 ga Nuwamban nan inda ya gaji tsohon Kwamishina Ahmed Iliyasu wanda aka yi wa karin girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar na  ’Yan sandan Najeriya.