Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

’Yan sanda za su shiga yajin aiki a Mali

Shugaban Qasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta

’Yan sandan kasar Mali sun lashi takobin shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani da kuma shirya gagarumar zanga-zangar nuna bacin ransu a ranakun 18 da 19 ga watan Maris wato makon gobe idan har ba a biya musu bukatunsu ba.

’Yan sandan sun fitar da wata sanarwa ta musamman a wani taron manema labarai da shugabannin kungiyar jami’an tsaron Mali suka shirya don yi wa gwamnatinsu barazana, kamar yadda kafar labarai ta TRT ta rawaito daga shafin sadarwa ta Intanet ta Malijet.

ADVERTISEMENT

’Yan sandan sun fadi bukatu 15 da suka hada da mallaka wa kowane daga cikinsu bindiga da alawus na daukar dawainiyar iyalansu da kuma bai wa takwarorinsu kudin goro sakamakon ruwa-da-tsaki da suka yi a zaben Shugaban Kasar.

Idan har ba a biya wadannan bukatu ba, ’yan sandan sun nuna cewa sun dauki niyyar yin zaman dirshan a kofar Babbar Hedkwatar ’Yan sandan Kasa a ranar 18 ga watan Maris da kuma Ma’aikatar Tsaro da Kare Fararen hula washegari.

ADVERTISEMENT

A wadannan ’yan makwannin, Mali na ci gaba da fama da koke-koke masu dmbin yawa daga sassa daban-dabban na al’umarta.