✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan bogi ne suka kawo rudani a zaben Bayelsa da Kogi – Sufeto Janar

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ce ’yan sandan bogi ne suka kawo rudani a zaben Gwamna da aka gudanar a ranar…

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya ce ’yan sandan bogi ne suka kawo rudani a zaben Gwamna da aka gudanar a ranar Asabar a jihohin Bayelsa da Kogi.

Alhaji Mohammed Adamu ya bayyana haka ne a fadar Shugaban Kasa, lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi, bayan taron da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi da manyan jami’an tsaron kasar nan, ya ce dukkan jami’an tsaron da aka tura wajen zaben suna da wata lamba ta musamman.

Ya ce tuni an kama mutum 11 da ake zargin suna da alaka da yamutsin da ya faru a lokacin zaben, kuma domin tabbatar da ainihin abin da ya faru an ci gaba da gudanar da bincike. Ya kara da cewa jirgi mai saukar ungulu da aka gani yana jefa barkonon tsohuwa a lokacin zabe a Kogi, an yi haka ne domin kariya, kuma jirgin na yin sintiri ne domin hana masu satar akwati da kuma tada hankalin jama’a.

Hakazalika ya ce dama ’yan sanda sun shirya sosai domin zaben a jihohin biyu, saboda rundunar na sane cewa za a iya samun rikici a jihohin biyu. Ya ce bayan haka duk dan sanda ko sojan da ka gani sanye da kayan sarki, amma ba ya da wannan alama da aka bayar don wannan zabe, to na bogi ne, ko kuma ba ya cikin masu aikin zabe, domin muna sane cewa wadansu ’yan siyasa sun dinka kayan ’yan sanda da na soja, don haka muka bullo da wannan tsari na ba da wa ta alama ga jami’an da ke kula da aikin zaben.

Mohammed Adamu ya kuma bayyana cewa tun kafin zaben sun horar da jami’an a kan irin rawar da za su taka na samar da ingantaccen tsaro da kuma yin aiki yadda ya kamata.

Game da takaddamar daukar ’yan sanda dubu 10, cewa ya yi tuni wadanda aka dauka suka fara samun horo, tun kafin Hukumar Kula da Harkokin ’Yan sanda ta shigar da kara.