✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan Filato sun kama ’yan fashi da masu garkuwa da mutane  44

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta gabatar wa manema labarai gungun ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta gabatar wa manema labarai gungun ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifaffuka su 44 da ta kama a sassan jihar.

Da yake yi wa ’yan jarida bayani a hedkwatar runudunar da ke Jos, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Issac Akinmolode ya ce a kokarin rundunar na magance matsalar aikata miyagun laifaffuka a jihar ya sanya ta samu wannan nasara.

Ya ce  rundunar ta samu nasarar kama mutum 11 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, wadanda suka hada da Bashir Muhammed da Umar Adamu da Yusuf  Adamu da Mustafa Mohammed da Sha’aibu Ado da Dantani Umar da Sama’ila Saranu Shitu da Adamu Mohammed da Hashimu Ya’u da  Jibiro Damina  da kuma Abubakar Hassan.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa Bashiru Mohammed da Umar Adamu sun tabbatarwa rundunar cewa sun yi garkuwa da mutane da dama a wurare daban-daban na jihar. Ya ce mutanen sun bayyana cewa Yusuf Adamu da Hashimu Ya’u da Shu’aibu Ado da Mustafa Mohhammed  su ne suka yi garkuwa da mutane a gidajen ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Jihar Filato a  Haipang da wasu wurare a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Ya ce wadanda ake zargin sun tabbatar wa rundunar cewa su ne suke yawan yin garkuwa da mutane a kananan hukumomin Mangu da Barikin Ladi da cikin garin Jos da kewaye.

Ya ce Jibiro Damina da Dantani Umar sun tabbatar da cewa su ne suke yawan yin garkuwa da mutane a dajin Jingir da ke Karamar Hukumar Bassa.

Har ila yau ya ce rundunar tare da taimakon ’yan sintiri ta samu nasarar kama wasu ’yan fashi da makami su biyar da suka dade suna yi wa matafiya fashi a hanyar Jos zuwa Jingir. Wadanda aka kama su ne Nasiru Gambo da Abdullatif Abdulganiyu da Shamsu Isiyaku da Abel Maikarfi da kuma Felid Ajayi.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta kama ’yan fashi da makami hudu, wadanda suka kware wajen yin fashi da makami da suke amfani da kakin soja. An kuma kama su ne a lokacin da suka yi kokarin yin fashin wata mota a hanyar Old AirPort da ke garin Jos. Wadannan da aka kama su ne Mohammed Usman da Jesse Adamu da Yahaya Hamza da Abdullahi Sani.

Ya ce rundunar ta kama wadansu ’yan fashi da suka kware wajen fasa shaguna a Zarmaganda da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, wadanda aka kama su ne Pam Dabou da Andrew Enock.

Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike kan wadannan mutane da ake zargi za a gabatar da su a gaban kotu.