✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan Kaduna sun musanta yin garkuwa da mutum 13

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta musanta rahoton da ake ta yadawa a kafafen sadarwar yanar gizo, wanda ke cewa masu garkuwa da mutane sun…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta musanta rahoton da ake ta yadawa a kafafen sadarwar yanar gizo, wanda ke cewa masu garkuwa da mutane sun sake yin garkuwa da wasu mutum 13 a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Rundunar ta ce, ana yada wannan rahoton ne kawai don a tsorata matafiya hanyar.

Sai daki rundunar ta sanar da cewa, wasu ‘yan bindigar sanya da kayan sarki na soji inda suka shiga cikin wani gida a kauyen Dutse da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna ranar 23 ga Satumba 2019 da misalin karfe 1:30 suka sace mutum shida wanda har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna ya sanar.