✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sandan Sri Lanka sun kama masu kai wa Musulmi hari bayan hare-haren Easter

’Yan sandan kasar Sri Lanka sun kam mutum 20 da zargin kai hari ga gidaje da kuma shagunan Musulmi, abin da ya yi kama da…

’Yan sandan kasar Sri Lanka sun kam mutum 20 da zargin kai hari ga gidaje da kuma shagunan Musulmi, abin da ya yi kama da kokarin ramuwar gayyar harin bama-baman da wata kungiya ta kaddamar a lokacin bukuwan Easter, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 250.

An ga sojoji cikin motoci masu sulke na sintiri a garuruwan da rikicin bangarancin ya barke a makon nan, a yayin da jama’ar garuruwan musamman musulmi suke buya a cikin gonakin shinkafa don tsere wa gungun mutane masu dauke da miyagun makamai kamar adduna da kuma karafa, wadanda suka fusata da haren-haren kungiyoyin tsagerun.

Harin na ranar 21 ga watan Afrilu, wanda kungiyar IS ta yi ikirarin kaddamar da shi a kan otel-otel da kuma coci-coci, mafi yawa a birnin Colombo sun haifar da zaman zullumin, da tunanin tunanin ramuwar gayya a kan tsirarun al’ummar musulmin kasar da yawanci suke zama a tsibirai.

Al’ummar musulmi mazauna kasar sun ce gungun mutane dauke da muggan makamai sun shigo garuruwan Arewa maso Yammacin Sri Lanka a kan babura da motocin bas, inda suka rushe masallatai da kone littafan Al-kur’ani tare da far wa shaguna, ta hanyar amfani da baman-baman fetur, a rikicin da ya barke tun ranar Lahdi.

’Yan sanda dai sun ce sun kama mutum 23, a tsibirin bisa laifin tunzura tashin hankali kan al’ummar muslmin wadanda yawansu ke kasa da kashi 10 cikin dari na al’ummar Sri Lankar mutane miliyan 22, da galibinsu  mabiya addinin Buddha ne.

Kakakin ‘yan sandan kasar, Ruwan Gunasekera ya ce an shawo kan al’amarin, kuma ba a sake samun barkewar wani sabon tashin hankali ba.

Sri Lanka dai ta yi kaurin suna wajen samun tashe-tashen hankula masu nasaba da addini ko kabilanci, kuma yake-yaken basasa sun daidaita kasar, cikin gomman shekaru da aka shafe ana gwabzawa tsakanin ’yan awaren kabilar Tamil Tigers, marasa rinjaye da kuma ’yan Buddha, wadanda suka yi kane-kane a gwamnatin kasar.