✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan siyasa da Boko Haram na shirin ‘tarwatsa’ Zamfara – Gwamna

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fallasa cewa ta samu ‘rahotannin sirri’ dangane da kulle-kullen da wadansu ’yan siyasa ke yi domin su ‘tarwatsa’ Jihar Zamfara. Sai…

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fallasa cewa ta samu ‘rahotannin sirri’ dangane da kulle-kullen da wadansu ’yan siyasa ke yi domin su ‘tarwatsa’ Jihar Zamfara.

Sai dai kuma gwamnatin jihar, ba ta bayyana sunayen wadanda take zargi da wannan shirin da ta kira na tarwatsa Jihar Zamfara  ba.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Yusuf Gusau ya fitar, ta yi zargin cewa wadansu ’yan siyasa “na kulle-kulle tare da hadin baki da Boko Haram domin a rika kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hare-hare.”

Jami’in ya kara da cewa shirin da wadannan marasa kishi ke yi shi ne domin su lalata sulhun da aka cimma a jihar ta Zamfara.

Daga nan ya kara da cewa wadannan masu niyyar yin wannan mugun nufi sun yi shirin kai hare-hare a wasu kananan hukumomi bakwai a cikin jihar da kuma wasu wurare muhimmai da ke cikin Gusau, babban birnin jihar.

Kananan hukumomin da suka shirya kai wa hare-hare sun hada da Gusau, Tsafe, Talata Mafara, Anka, Zurmi, Maru da Maradun. Wurare biyu da aka shirya kai hari a birnin Gusau su ne Babban Masallacin Juma’a da kuma Kasuwar Barikin Sojoji.

An ce tuni wadannan ’yan siyasa suka dauki sojojin haya na ’yan Boko Haram da za su rika kai wadannan hare-hare.

Daga nan sanarwar ta ce wannan barazana ba za ta tauye wa Gwamna Bello Matawalle gwiwar ci gaba da samar da tsaro a fadin jihar ba.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadin yadda ’yan suka sake sakin wadansu mutum 30 da suka hada da maza 15 da mata 15.