✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan siyasa ke ruruta rikicin kabilanci – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya dora alhakin ruruwar rikicin kabilanci a kan ’yan siyasa da ke son cimma bukatunsu na son rai.…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya dora alhakin ruruwar rikicin kabilanci a kan ’yan siyasa da ke son cimma bukatunsu na son rai.

Sarkin Musulmi ya yi ikirarin ne a cocin Saint Dabid’s Cathedral da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo a ranar Lahadin da ta gabata, a wurin taron kwana biyu da Cibiyar Tuntuba Tsakanin Addinai (NIREC), ta shirya.

Ya shawararci ’yan Najeriya sun kaurace wa ’yan siyasa da masu hannu da shuni da ke tsoma rigar siyasa a harkokin addini.

Ya ce Alkur’ani Mai girma da Baibul ba su da alaka da kowace jam’iyya.

Dangane da rushe masallaci a Fatakwal da ake zargin gwamnatin Jihar Ribas da yi, ya ce tuni NIREC a matsayinta na uwa a kasa ta dauki alhakin lalubo hanyar samar da maslaha.

Sarkin Akure (Deji na Akure) Oba Aladetoyinbo Aladelusi ne gayyaci Sarkin Musulmi domin halartar taron da ake gudanarwa a kowace shekara don inganta al’adu.